Kuje Kotu Idan Baku Yarda Da Sakamakon Zaɓen Fidda Gwani — PDP Ga Ƴan Takara A Ogun

Kuje Kotu Idan Baku Yarda Da Sakamakon Zaɓen Fidda Gwani — PDP ga ƴan Takara a Ogun

Jam’iyyar PDP a Jahar Ogun tayi kira ga Fusatattun Ƴan Takarar Gwamna guda biyu dasu je Kotu tare da neman haƙƙin su, idan basu gamsu da sakamakon Zaben Fidda Gwani da aka gabatar a ƴan kwanakin nan.

Dayake jawabi ga Manema labaru a Sakatariyar Jam’iyar dake Abeokuta, Babban Birnin Jahar Ogun, Shugaban Jam’iyyar Sikirulahi Ogundele yayi kira ga ƴan Takara Segun Showunmi da Jimi dasu sanya Jam’iyyar a cikin zuciyar su.

Ogundele ya ayyana Fusatattun Ƴan Takarar dake cewa sun samu nasara a matsayin masu neman tada zaune tsaye.

Yace Dan Takarar da aka zaba a PDP a Jahar Ogun shine Oladipupo Adebutu, kuma babu wani sai shi.

Showunmi a ranar 25 aka gudanar da zaɓen fidda Gwani inda aka zaɓe shi a matsayin Ɗan Takarar Gwamna.

Lawal, wanda ya jagoranci Zaben Fidda Gwani daya fitar da Adebutu a matsayin Ɗan Takarar, yayi kira da aka soke zaben a Jahar, yana mai cewa sunayen Deliget da aka yi amfani dasu wajen zaɓen bana gaskiya bane.

Amma Jam’iyyar PDP tace bata yi wani zaɓen fidda Gwani guda a ko’ina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram