Zamu Cigaba Da Kare Ƴan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje – Buhari

Zamu Cigaba Da Kare Ƴan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje — Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a Kasar Madrid, yace Gwamnatin Tarayya zata yi rige-rige wajen kare ƴan Najeriya mazauna Ƙasashen waje.

Buhari ya bada umarnin a lokacin da ya gana da ƴan Najeriya mazauna Ƙasar Spain a ziyarar sa daya kai na kwanaki uku.

A cewar sanarwar da Mai bashi Shawara ta Fuskar Kafafen Yaɗa Labaru Femi Adesina, tawagar ƴan Najeriya wadda ta gana da Shugaba Buhari, daya haɗa da Shugaban Ƙungiyar John Bosco, Mataimakin sa Richard Omoregbe, Ɗan wasan Super Eagles da yake wasa a Spain a Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Madrid Kenneth Omeruo, da Obinna Okafor, da Dalibin koyan Sufurin Jirage Mohammed Bashir, da Segun Adedoyin, da Dan Kasuwa Bright Omorodion.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shaidawa ƴan Najeriya cewa sune Jakadun Ƙasar yace “da yawan ku kuna wannan ƙasa a dalilai daban-daban, musamman a wasanni inda kuke samun abun da kuke rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram