APC Ta Ce Sai Ta Hukunta Tinubu Saboda Kalaman Rashin Ɗa’a Da Ya Yi Ga Buhari

Shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa sun bayyana matsayarsu ta kin karɓar uzurin da jagoran jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu ya bayar game da kalaman da ya yi da ake tuhumarshi da rashin ɗa’a ga shugaba Buhari.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa uwar jam’iyyar ta ce takardar bada haƙuri da Tinubu ya rubuta ba zata isa a bar maganar ba face jam’iyya ta hukunta shi.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne dai jigon jam’iyyar, Tinubu ya yi wasu kalamai inda ya ce ba don shi ba da Shugaba Buhari bai samu mulki ba a 2015 maganar da ta janyo kace-na-ce a faɗin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram