Bayan Yasha Ƙasa A Zaɓen Fidda Gwani Na Shugaban Ƙasa, PDP Ta Ba Gwamna Bala Tikitin Tsayawa Takarar Gwamna

An ayyana gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar.

A yau ne aka sake zaben fidda gwani a otal din Zaranda da ke Bauchi.

Kuma Shugaban kwamitin zaben Murtala Damagum a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben ya bayyana cewa akwai wakilai 656 a jihar.

Ya bayyana cewa 20 daga cikin wakilan akwai wakilai na kasa daga kowace karamar hukuma 20 na jihar.

Damagum ya kara da cewa sauran wakilai 636 da suka rage a gundumomin zabe 323 na jihar.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Damagum, ya ce wakilai 10 ba su halarta ba, 650 kuma suka samu amincewa yayin da wakilai 646 suka kada kuri’a.

A cewarsa, gwamna Mohammed ya samu kuri’u 646 da aka kada.

A jawabinsa na godiya, Mohammed ya bayyana godiyarsa ga sakataren gwamnatin jihar, wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna na farko da aka gudanar a makon da ya gabata, amma ya sauka domin kauran Bauchin ya hau.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa an ayyana Ibrahim Kassim a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna na farko da aka gudanar a makon jiya amma ya sauka domin share fagen zaben ga gwamna Mohammed.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram