Dole Gwamnati Tayi Gaggawar Sakin Ɗiyan Ƴan ta’adda, domin Ceto Namu – Abdulfatah Jimoh

Shugaban iyaye da da yan’uwan wadanda aka sace yayin harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna Dr Abdulfatah Jimoh yayi kira ga Gwamnatin tarayya kan ta gaggauta biyan bukatun wadanda suka yi garkuwa da yan’uwan su.

Dr Abdulfatah ya yi wannan kiran ne yayi wata hira ta musamman da Jaridar Punch tayi da shi a karshen Mako, kan halin da yan’uwan wadanda aka yi garkuwa da su suke ciki.

A cewar sa yau kwanaki 68 ke nan da garkuwa da yan’uwan su, amma har kawo yau babu wani ci gaba da aka samu kan kokarin ceto iyalan nasu.

Da aka tambaye shi kan ko bata garin sun tube su ta waya kan batun kudin fansa?

Dr Jimoh ya ce eh wani lokaci a baya sun tuntube su kan batun kudin fansa, inda suke gaya musu cewa su zama cikin shirin domin zasu dawo gare su, domin gaya musu farashin da zasu biya domin su karbi yan uwansu cikin koshin lafiya.

Yanzu haka dai tuni aka yan garkuwar suka saki wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su din, kuma a cewar Dr Jimoh yanzu haka akwai ragowar mutane 61 a hannun yan Garkuwan.

A karshe Dr Jimoh ya bukaci gwamnatin tarayya kan ta saki wadanda yan garkuwan suke bukata a sakar musu domin suma su sadu da yan’uwansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram