Idan Ya Dawo Daga Balaguro Ghana, Buhari Zai Gana Da Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ana saran zai yi taro da Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa na APC a ranar Lahadi.
Shugaban Ƙasa na Shirin yin tafiya zuwa Ƙasar Ghana a Yau (Asabar) ba tare da fito da Ɗan takara wanda hakan ke cigaba da haifar da rikici a cikin Jam’iyyar.
Wani daga cikin Kusar Gwamnati daya buƙaci a sakaye sunan sa, ya shaidawa Majiyar mu cewa Shugaban Ƙasa zai dawo a yau.
Duk da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daya dawo daga Ƙasar Spain a ranar Juma’a da rana, ana saran zai gana da ƴan Takara da daddare a ranar Asabar ko Lahadi.
“Shugaban Ƙasa ana saran zai yi tafiya zuwa Ghana (yau). Bayan haka ana saran zai yi taro da Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa, kuma zai sanar masu da wanda yake so Jam’iyyar ta baiwa Tikitin Takara”, Inji Majiyar tamu.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari dai a ranar Talata ya gana da Gwamnonin Jam’iyyar APC gabanin Babban Taron ta na Ƙasa.
Mai ba Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari shawara na musamman akan Kafafen Yaɗa Labaru Femi Adesina ya sanar da abinda aka tattauna a taron.
A lokacin taron daya gudana a Abuja, Buhari ya gayawa Gwamnoni cewa matsayar sa shine a zaɓi Dan Takarar da zai sanya Jam’iyyar ta cigaba da mulkin Ƙasar.
Taron yazo bayan raɗe-raɗi da ake cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai sanar da Ɗan Takarar sa kafin Babban Taron.