INEC Ta Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Wa’adin Miƙa Sunayen Ƴan Takara

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya shawarci jam’iyyun siyasa da su kiyaye dangane da wa’adin mika sunayen ‘yan takara a babban zaben 2023.

Farfesa Yakubu ya bayar da shawarar ne a jiya Juma’a a lokacin da ya ziyarci wurin wani taron horo da hukumar ta shirya wa jami’an jam’iyyun siyasa na kasar nan.

Taron Horaswar dai zai mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da sabuwar hanyar mika sunayen yan takara (ICNP) a zaben 2023.

Yakubu, a cewar sanarwar da babban sakataren yada labaran sa, Mista Rotimi Oyekanmi ya fitar, ya ziyarci dukkanin kungiyoyi shida da ake bayar da horon domin tabbatar da cewa jami’an jam’iyyar sun fahimci abin da ake koya musu.

Shugaban na INEC ya bukaci jami’an da su lura da su a hankali dangane da ranakun da za su fara aiki da wa’adin ranar da za a fara gabatar da fom din ‘yan takara na zaben kasa da na jihohi zuwa hukumar.

Yakubu ya tunatar da jami’an jam’iyyar duk wasu bayanai da ke kunshe a cikin jadawalin ayyuka na babban zabe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram