Mutane Biliyan 1.5 Ke Buƙatar Abinci, Da Taki — UN Ta Koka Yayin Da Yaƙin Ukraine Ya Shiga Kwanaki 100

Mutane Biliyan 1.5 ke buƙatar Abinci, da Taki — UN ta koka yayin da yaƙin Ukraine ya shiga kwanaki 100

Jami’in dake Kula da Bayanan Faɗan Ukraine na Majalisar Dinkin Duniya Amin Awad ya bayyana cewa kimanin mutane biliyan 1.5 a faɗin duniya ke buƙatar Abinci da Takin Zamani, a yayinda yaƙin Russia-Ukraine ya shiga kwanaki 100.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana haka a ranar Juma’a, inda tace Awad ya bayyana haka ga Ƴan Jarida a Geneva daga birnin Kyiv na Ƙasar Ukraine.

Yace UN na bakin Ƙoƙari na ganin ta fito da kayan abinci ta Jirgin Ƙasa, da kuma Taki daga Russia, sannan ana bakin ƙoƙarin aga idan rufe tashoshin ruwa za’a dawo dashi, domin shigo da taki da kayayyakin abinci su wadata.

“Muna cigaba da tattaunawa. Akwai matsaloli musamman tsakanin Moscow da sauran Ƙasashe wanda suka nuna damuwar su, kuma ake cigaba da tattaunawa. Amma har yanzu ba’a cimma matsaya ba”, Inji Awad.

Yace suna aiki da Bankuna domin ganin yadda za’a riƙa cinikayya da Russia musamman ta fuskar kudi ya dawo”.

“Kimanin mutane Biliyan 1.5 ke buƙatar Abinci a faɗin duniya. Ina fata tattaunawa zata tafi yanda ya kamata da zaran an fara, domin ganin an dawo da cinikayya ta abinci da Taki, kafin wani rikicin kuma”, Inji shi.

“A yau, kimanin mutane Miliyan 15.7 a Ukraine na Buƙatar taimako da kariya. Kullum ƙara yawa suke yi, kuma faɗa na cigaba da wakana, rayuwa dubbannin mutane na cikin tasku”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram