Ƴan Ƙungiyar Asiri 4 Sun Mutu, Yayin Raba Kuɗin Da Ƴan Siyasa Suka Basu A Bayelsa
Kimanin mutane hudu ne rahotanni suka ce sun rasa rayukansu a Swali na Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, yayin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka yi artabu kan rabon kudaden da ‘yan siyasa daga yankin suka bayar.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da al’ummar Yenagoa suka sanya dokar hana ayyukan asiri a yankin.
A cewar wata majiyar al’umma, wadanda aka kashe ana zargin ‘yan kungiyoyin asiri biyu ne da ake kira ‘Dey-riji da Bobos’.
Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa yayin da aka kashe mutane uku a unguwar Swali, an harbe daya da safiyar Lahadi a kan hanyar Osiri, unguwar Ekeki na Yenagoa.
Rikicin baya-bayan nan na kungiyar asiri a birnin Yenagoa ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna birnin, wadanda galibin lokuta suke zama a gida don gudun kada a yi musu fashi.
Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar Bayelsa da ta dauki lamarin tsaro da muhimmanci tare da dakile tashe-tashen hankula a jihar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya ce jami’ansu sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a rikicin kungiyar.
Sai dai ya ce ‘yan kungiyar asiri biyu ne suka mutu a yayin rikicin.
Ya ce, “Mun kama mutane hudu da ake zargi da hannu a rikicin kungiyar, yayin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka mutu a rikicin. Ana ci gaba da bincike.” inji shi.