Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Ana cigaba da zaman ɗar-ɗar a mahadar Uti ta Effurun dake karamar hukumar Uvwie ta jahar, inda yan bindiga suka samu nasarar harbe jami’in da aka ɗauko akan babur,sannan sukayi nasarar guduwa da bindigoginsa.
Wasu daga chikin wadanda suka tabbatar faruwar lamarin sun shaida cewa, direban Babur ya samu matsanacin Raunuka a sanadiyyar Harbin.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, mamacin jami’in yana ɗauke da bindigu biyu ne, sakamakon daya ta Abokin aikinsa wanda ya bar wurin aikinsa, a yayinda dayar kuma tasa ce.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa,mutanen da suka tabbatar da faruwar lamarin sunyi gudun ceton rai domin tseratar da rayukansu .
Jami’in hulda da jama’a na Rundunar yan sandar jahar, DSP Bright Edafe ba’a same shi ba domin jin ta bakinsa, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.