Da Ɗumi-Ɗumi: Mataimakin Gwamnan Oyo Ya Fice Daga PDP Zuwa APC
Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan, a ranar Lahadi, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress wato APC .
Sanarwar ficewar sa daga jam’iyyar PDP ta fito ne a ofishinsa mai zaman kansa da ke Ojoo, Ibadan, yayin da yake zantawa da manema labarai.
Sanarwar tasa ta biyo bayan rade-radin da ake yi na cewa zai fice daga jam’iyyar ne saboda rashin jituwar da ke tsakaninsa da maigidan sa Gwamna Seyi Makinde.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai wasu rahotanni suka bayyana cewa Makinde ya ajiye Olaniyan a matsayin mataimakinsa a zaben gwamna na 2023 amma ba a fitar da wata sanarwa a hukumance kan hakan ba.
A shekarar 2020 ne mataimakin gwamnan ya kai kara ga kwamitin da Dr. Saka Balogun ya jagoranta domin sulhunta ‘yan PDP da suka ji ra’ayi, cewa Makinde ya yi watsi da shi na tsawon lokaci.