Da-Dumi-Dumi: Yan bindiga Sun Sake Garkuwa Da Mutane 14 A Kaduna

Da-Dumi-Dumi: Yan bindiga Sun Sake Garkuwa Da Mutane 14 A Kaduna

Wasu ‘yan bindiga da suka addabi jihar Kaduna a safiyar Asabar sun yi garkuwa da mutane 14 a wata unguwa mai suna Iri Station mai tazarar kilomita 8 daga garin Idon, na karamar hukumar Kajuru ta jihar.

Da yake tabbatar da hakan ga jaridar Sun Newspapers, jimi’i mai kula da harkokin kudi da lafiya na karamar hukumar Kajuru, Bala Jonathan ya bayyana sunayen wadanda aka sacen da suka hada da Abdullahi, Yakubu Isah, Samson Julius, Angelina Julius, Pasema Daniel, Junior Julius.

Sauran sun hada da Bobo Julius, Saratu Mohammed, Asenath Sunday, Confidence Jerry, Barnaki Sunday, Moses Kenneth, Danladi Goma da Ummi Jibrin.

“Wadannan su ne sunayen mutanen da aka sace a tashar Iri da aka gano a yanzu. Abin bakin cikin ya faru ne da sanyin safiyar yau, 4 ga Yuni, 2022,” in ji Jonathan.

A cewar jami’in har yanzu wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a baya suna nan tare da ‘yan bindigar saboda ‘yan uwansu da al’ummarsu ba su samu damar biyan kudin fansan wadanda suka sace su ke nema ba.

Batun sace-sacen jama’a a unguwar Idon da ke Kajuru da kewaye ya zama ruwan dare gama gari wanda ya janyo wa al’ummar da abin ya shafa cikin halin kaka-nika-yi, wadanda suka yi watsi da rayuwarsu da amfanin gonakinsu domin biyan kudin fansa don kwato ‘yan uwansu daga ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, wadanda suka yi musu rauni yadda suka ga dama.

Bayyanan sirri daga yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun rika kai munanan hare-hare a kan al’umomin da ba su da laifin komai daga wannan wuri da ke kusa da Ungwan Makeri ta Mokoro Zankariya, na gundumar unguwar Idon a Kajuru ba tare da wani martani daga gwamnatin jihar da jami’an tsaro ba, na tabbatar da tsaro da rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin ba.

A cikin wannan shekarar kadai, an yi garkuwa da daruruwan mutanen yankin a Ungwan Makeri, garin Idon, Idon Hanyi, Agunu Dutse, Sabon Gari Kufana a cikin Kajuru da dai sauran su a kananan hukumomin Kajuru da Kachia da ke makwabtaka da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram