Rundunar Yan sanda Ta Tabbatar Da Fashewar Wani Abu A Cocin Katolika Na Ondo
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da fashewar wani abu a cocin St Francis Catholic dake kan titin Owa-luwa a karamar hukumar Owo ta jihar.
DAILY POST ta ruwaito cewa wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba sun mutu sakamakon fashewar wani abu da ya faru a harabar cocin.
Lamarin wanda ya faru a yau Lahadin a lokacin ibada, ya haifar da tashin hankali a yankin inda aka ce wasu mazauna garin sun fice daga garin domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.
Ko da Jaridar DAILY POST ta tuntubi, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, DSP Odunlami Ibukun, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Jami’ar wadda ta zanta da wakilin Majiyar Jaridar Jakadiya yayin da take wurin da fashewar ta auku domin tantancewa a wurin, ta ce nan ba da jimawa ba za a yi bayani kan adadin wadanda suka mutu a cikin wata sanarwa.
Ta ce, “a halin yanzu muna wurin da lamarin ya faru domin samun adadin barnar da aka yi. Ba kamar abin da ke faruwa a shafukan sada zumunta ba. Nan ba da jimawa ba za mu fitar da sanarwa don ba ku cikakken bayani kan abin da ya faru.”