Sakamakon Ƙin Ƙara Wa’adin Rajistar Katin Zaɓe, SERAP Ta Maka INEC Kotu

Kungiyar SERAP mai fafutukar ganin an samar da shugabanci na gari, da kuma wasu ‘yan Najeriya 185 sun shigar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), kara.

Masu karar dai na bukaci kotun da ta bayyana rashin bin ka’idojin kasa da kasa na gazawar hukumar zabe, wajen kara wa’adin rajistar masu zabe.

A cewar masu karar hakan ne zai baiwa ‘yan Najeriya da suka cancanta damar amfani da ‘yancinsu.

Dangane da matakin da ta dauka a baya, INEC ta kara wa’adin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa da kwanaki shida, daga ranar 3 ga watan Yuni zuwa 9 ga watan Yuni

Wa’adin rijistan masu kaɗa ƙuri’ar (CVR) zai kare ne ranar 30 Yuni 2022.

A cikin karar mai lamba FHC/L/CS/1034/2022 da suka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman kotun da ta tantance “ko gazawar INEC na tsawaita wa’adin rajistar masu zabe bai saba wa ‘yan Najeriya ba.

‘Yancin jama’a na shiga cikin gwamnatinsu wani muhimmin abu ne na kowace al’umma ta dimokuradiyya, kuma duk wani tauye hakkin da bai dace ba zai shiga zuciyar gwamnatin wakilai.”

Kotun dai bata bayyana ranar da za ta fara sauraren karar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram