Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da yammacin Jiya Asabar yayin da ake yi ruwan sama a yankunan Ngwo da Sabuwar Kasuwa na jihar dake a karamar hukumar Enugu ta Arewa.
Lamarin, abin takaici, an ruwaito cewa ya shafi ma’aikatan da ke cikin tashar a lokacin da lamarin ya faru.
Wani ma’aikacin gidan rediyon da ya tabbatar da faruwar lamarin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, lamarin ya sanya a karo na hudu da tsawar tana afkawa tashar.
Ma’aikatan sun ce abokin aikin su da abin ya shafa, Humphrey, dan jaridan Wasanni, a zahiri baya bakin aiki amma saboda yana zaune a kusa da gidan rediyon yakan zauna har sai an rufe tashar a kowane dare.
”Ya suma kafin a garzaya da shi asibiti, amma mun gode Allah ya dawo hayyacinsa.” a cewar Ma’aikatan.
Yanzu haka dai An sallame shi a safiyar yau Lahadi.
Gidan rediyon da ke watsawa shirye shiryen da akan Mita 99.9FM yana saman tudun Ngwo, karamar hukumar Enugu ta Arewa.
Duk Kokarin jin martanin shugaban gidan rediyon, Family Love FM, Mista Celestine Ugwuanyi, ya ci tura domin ba a iya samunsa ta wayar tarho har kawo lokacin haɗa wannan rahoton.