An Fi Son Sususu Talasuru Raƙumi Da Akala Wadda Za A Juya Yadda Ake So – Mustapha Inuwa

Tsohon Sakataren Gwamnatin jahar Katsina kuma tsohon ɗan takarar Gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Mustapha Muhammed Inuwa ya bayyana cewa mutanen da ke goya ma shi baya su yi hakuri da abinda ya faru game da zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamna da jam’iyya APC ta yi a jahar Katsina.

Mustapha ya bayyana haka ne a yayin wani taro da ya yi da wakilan kungiyoyi masu goyon bayanshi a faɗin jahar Katsina, a ɗakin taro na Katsina Motel a ranar Lahadin nan.

Tsohon Sakataren gwamnatin ya ce kwarai da gaske abin da ɗaci amma idan suka duba yadda abin ya taso dama da manufa aka yi shi.

Ya ce abinda akai ya nuna ƙaƙara cewa an fi son a samu sususu wanda za a juya shi yadda ake so.

Ya ƙara da cewa shi kuwa kowa ya sani ba a iya juya shi si yasa aka yi abinda aka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram