Babu Dalilin Cin Zarafin Ƴan Arewa Mazauna Kudu – Inji Shehu Sani

Biyo bayan wani mummunan hari da wasu ‘yan ta’adda suka kai wa mabiya Coci a garin Owo na jihar Ondo, tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi gargadi kan cin mutuncin ‘yan Arewa mazauna Kudu.

Shehu Sani ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin a shafinsa na Twitter, inda ya ce manufar ‘yan ta’addar ita ce ta haifar da barna da rigingimun kasa.

“Ba sa barin masu ibada a cikin masallatai ko a coci-coci. Arewa ce ke fama da tashe-tashen hankula a kullum,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sai dai a baya Sanata Shehu Sani ya yi Allah-wadai da harin da aka kai a cocin Katolika na Ondo, yana mai bayyana hakan a matsayin wani mummunan aiki na ta’addanci, da dabbanci da kuma abin la’akari.

“Dole ne dukkan ‘yan Najeriya su hada kai wajen yin tir da wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

Dole ne a yi duk abin da za a gabatar da maharan. Ya isa wannan zubar da jini,” ya rubuta.

Al’amarin da ya faru a Cocin Owo, wanda shi ne hari na baya-bayan nan a Najeriya, na ci gaba da yin tofin Allah tsine daga ciki da wajen kasar, inda ake ta kiraye-kirayen hukumomi da su yi abin da ya kamata wajen kare martabar rayuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram