Da-Dumi-Dumi: Gwamnonin Arewa Sun ƙi Amince Wa Da Ahmad Lawan, Sun Dage Kan Fito Da Ɗan Takara Daga Kudu

Gwamnonin Arewa Sun ƙi Amince Wa Da Ahmad Lawan, Sun Dage Kan Fito Da Ɗan Takara Daga Kudu

Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya yi wa manema labarai karin haske a fadar Shugaban kasa da ke Abuja ranar 6 ga Yuni, 2022.

Gwamnan ya ce Gwamnonin Arewa da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC sun dage cewa za su marawa dan kudu baya don ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki a zaben 2023 mai zuwa.

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Gwamnonin, 13 daga cikinsu, sun bayyana matsayarsu ne bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Gwamna Lalong, a cikin jawabinsa, ya yi karin haske kan cewa bayanan da aka bankado da aka yi ta yadawa a ranar Asabar da ta gabata, shi ne hakikanin matsayin gwamnonin Arewa kuma sun zo ne domin tuntubar shugaban kasar a hukumance.

A cewar gwamnan, shugaba Buhari bai nada ko daya daga cikin ‘yan takara 23 da ake sa ran za su shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar a matsayin dan takarar jam’iyyar APC ba.

Maimakon haka, ya bayyana cewa shugaban kasar ya bukaci gwamnonin da su yi taro da kwamitin zastaswa na jam’iyar (NWC) don warware matsalar dan takarar da ya dace ta hanyar dimokuradiyya.

Gwamna Lalong ya bayyana cewa matakin da gwamnonin suka dauka na mayar da mulki yankin Kudu shine tabbatar da daidaito, zaman lafiya da hadin kai a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram