Deliget 2,340 Ne Zasu Zaɓi Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam’iyyar APC

Deliget 2,340 Ne Zasu Zaɓi Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam’iyyar APC

A ƙalla wakilan jam’iyyar APC masu zaben dan takarar shugaban 2,340 ne ake sa ran zasu kada kuri’a a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyar APC.

Taron dai zai gudana ne yau a filin taro na Eagles Square dake daura da fadar shugaban Kasa a Birnin tarayya Abuja.

‘Yan takarar 23 da uku ne zasu fafata a zaben da ake saran fidda mutum guda wanda zai yiwa jam’iyar ta APC takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

Manyan “yan takarar da ake ganin zasu fafata a zaben na yau sun hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo da tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Ahmad Tinubu, da gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, da ministan sufuri Rotimi Amechi, da kuma wasu mutum tara.

A cewar shugaban jam’iyar ta APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu, ya ce tuni shirye-shirye suka kammala kuma jam’iyyar zata yi taron fidda gwani da ba a taba yin irinsa ba.

Ya kuma ce an fitar da kwamitoci daban-daban guda goma sha tara (19) da zasu tabbatar da zaben ya kammala cikin nasara.

Rahotanni dai sun bayyana cewa har zuwa daren jiya Lahadi jagororin jam’iyar ta APC na tattaunawa don yin masalaha kan dan takara guda daya da zai yiwa jam’iyar takarar shugaban kasa sai dai ba akai ga cimma matsaya ba, har kawo lokacin haɗa wannan rahoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram