Harin Ondo: Tinubu Ya Bada Kyautar Miliyan 75, Ya Buƙaci A Ƙara Tsaro

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, kuma dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi alkawarin yin aiki tare da Gwamna Rotimi Akeredolu domin kawo agaji ga wadanda rikicin Owo ya shafa.

A yayin da yake jawabi yau Litinin a fadar Olowo, Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye a ziyarar jaje tare da Akeredolu, Tinubu ya yi Allah-wadai da mummunan harin da aka kai wa masu ibada da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya bayyana harin a matsayin wani mugun abu da ya kamata a yi nasara a kansa, yana mai cewa “babu inda za a yi irin wannan kiyayya da kashe rayukan da ba su ji ba ba su gani ba” a kasarmu su ci gaba da wanzuwa.

Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki cocin St. Francis Catholic Church a garin Owo a ranar Lahadin da ta gabata inda suka kashe sama da mutane 30 wadanda galibi yara ne mata.

Kafin ya ziyarci cocin Tinubu ya yi alkawarin bayar da Naira miliyan 50 ga wadanda abin ya shafa, sannan kuma ya ba wa Cocin Katolika ta Owo Naira miliyan 25.

A yayin da yake bayyana bakin cikinsa kan wannan mummunan lamari, Tinubu ya bayyana cewa yankin Kudu-maso-Yamma ba su taba ganin an kai hari mai girman irin wannan ba yana mai cewa abin tsoro ne.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su hada kai don karfafa tsaro a fadin kasar nan.

Anasa bangaren Gwamnan jihar Akeredolu, ya yabawa Tinubu kan dakatar da ayyukan yakin neman zabensa na shugaban kasa kasa da sa’o’i 24 gabanin babban taron jam’iyyar APC, tare da zuwa domin jajanta musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram