Jami’an Tsaro Sun Ƙwato Manyan Makamai Daga Ƴan Bindiga A Jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi

Jami’an Tsaro Sun Ƙwato Manyan Makamai Daga Ƴan Bindiga A Jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi

 

Runduna ta 8 ta sojojin Najeriya dake Sokoto, a ranar Litinin, ta mika bindigogi iri-iri har guda 706 da aka kwato daga hannun ‘yan bindiga zuwa cibiyar kula da kanana da kananan makamai.

A wani takaitaccen biki da aka gudanar a barikin Giginya dake Sokoto, babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Uwem Bassey, ya bayyana cewa kwato kayayyakin na daga cikin shirin da ake yi na tabbatar da dakile hare-hare mai suna “Operation Hadarin Daji”.

A cewarsa, farmakin da ya aka kama a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina da Kebbi, an yi nasara ne domin kawar da ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka daga wadannan jihohin tare da kwato makamansu.

“Kuma muna kan hanya ne saboda mun fatattaki tsaunin Bakura, dajin Gundumi da sauran maboyar ‘yan bindiga a Jibia da dai sauransu. Kuma a yau muna mika makaman da muka kwato daga wadannan samamen” inji shi

Ya bayyana cewa, wannan farmakin ya kunshi dukkan jami’an soji da ‘yan sanda da kuma DSS, kuma ana ci gaba da gudanar da aikin ne saboda makiya wannan kasar.

“Ba za mu gaji da bin su ba. Za mu ci gaba da toshe hanyoyin mashigar su tare da yi musu kwanton bauna,” ya kara da cewa.

Ya nemi a ba da sahihan bayanai don ba da damar sojoji su kawo karshen barazanar.

Bassey ya kuma bukaci masu aikin yada labarai da su kasance da kishin kasa a duk lokacin da suke bayar da rahoto.

“Saboda idan ba tare da zaman lafiyar Najeriya ba, ba za ku iya yin sana’ar ku ba,” in ji shi.

Da yake karbar kayayyakin, Kodinetan shiyyar na cibiyar mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Air Vice Marshall Mohammed Haruna ya yabawa rundunar bisa samun nasarar wannan aikin.

“Wannan ya nuna cewa aikin yana samun gagarumar nasara don haka muna rokon ku da ku Kara kaimi” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram