Jami’ar Ta Kori Farfesa Biyu Kan Cin Zarafin Ɗalibai

Shugaban jami’ar Abuja Farfesa Abdul-Rasheed Na Allah ya ce jami’ar a shirye take domin daukar mataki mai tsauri kan duk wani malami da aka samu da laifin cin dalibar sa.

Na Allah yace yanzu haka akwai Farfesa gida biyu da aka Kore su daga bakin aiki gaba daya sakamakon kama su da laifin makamancin haka.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai yau s Birnin New York na kasar Amurka, inda yace tuni suka samar da tsarin yaki da wannan dabi’a kuma sun wallafata yadda kowa zai gani.

Na Allah dai na kasar Amurka yanzu haka, inda yake ziyarar kwanaki biyu da nufin ganawa da tsofaffin daliban jami’ar dake can.

Ya ce sunyi hakan ne da nufin samar da kariya ta musamman ga matan dake karatu cikin wannan jami’a wanda hakan zai basu kwanciyar hankali ci gaba da karatun su yadda ta kamata.

A karshe yace jami’ar su zata ci gaba da sanya idanu kan malamai da dalibai, da nufin tabbatar da cewa ba a samu damar cin zarafin kowanne daga cikin su bah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram