Ƴan Sanda Sun Gano Bama-bamai A Cocin Da Aka Kai Harin Ondo

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya bayyana cewa an gano wasu bama-bamai daga wurin da aka aki harin a cocin St. Francis Xavier Catholic, Owo dake jihar Ondo a ranar Lahadi.

Alkali Baba wanda ya yi Allah-wadai da wannan mummunar aika-aika ya ce wasu daga cikin wadanda suka aikata wannan aika-aika sun yi kama da masu ibada.

“’Yan bindigar, daga binciken farko, sun mamaye cocin da makamai da kayan da ake zargin bama-bamai ne.

‘Yan sanda “Masu bincike wadanda ke cikin wadanda aka tura wurin da lamarin ya faru sun kwato kwalayen alburusai na AK-47, da kuma kayayyakin abubuwan fashewar sinadarai da na’urori masu fashewa (EOD-CORNE) wanda suka tabbatar da amfani da bama-bamai a matsayin guntayen na IEDs. Inda akayi amfani da su kuma bayan share fagen da aka yi sosai, an gano wasu bama-bamai guda 3 da ba su tashi ba a wurin da lamarin ya faru.

“Bincike da aka yi ya nuna cewa wasu ‘yan bindigar sun shiga cikin cocin, yayin da wasu ‘yan bindiga da suka boye kansu a kusa da harabar cocin daga wurare daban-daban, suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.”

IGP din ya ci gaba da cewa, “An gano cewa maharan sun gudu ne ta hanyar amfani da wata mota kirar Nissan Sunny mai lamba AKR 896 AG da suka kwace daga hannun mai gidan, inda suka tsere ta hanyar Owo/Ute.

Sannan yace an gano motar yayin da mai motar ke taimakawa ‘yan sanda a binciken da suke yi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram