A yayin fara jawabin yan takara Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi ne mai neman takara na farko da ya soma jawabi.
Ya ce a shirye yake da ya soma aiki daga ranar farko da ya zama shugaban ƙasa.
Kamar yadda BBC ta ruwaito ta ce ya kuma bayyana cewa shi mai ɗaukar abubuwa da gaske ne kuma bai zo da wasa ba. Ya kara da cewa shi mutum ne mai son haɗin kan ƙasa.
Ya bayyana cewa a shirye yake domin ya yi wa Najeriya aiki.