Da Ɗuminsa: Kwankwaso Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani Na NNPP
Tsohon Gwamnan Jahar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya samu nasarar lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyya mai alamar kayan marmari daya gudana a ranar Laraba.
Jam’iyyar NNPP a halin yanzu tana Gudanar da zaben fitar da Gwani a Filin Wasa na Velodrome na Moshood Abiola Dake Abuja.
Kwankwaso ya samu nasarar lashe Zaɓen bayan Deliget sun nuna amincewar su ta hanyar murya ɗaya.