Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan a ranar Laraba ya bayyana cewar samun nasarar Asiwaju Bola Tinubu a matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, ya tabbatar da nasarar Jam’iyyar a Shekarar 2023.
A cikin wata takarda daya sanyawa hannu, Lawan wanda ya kasance Ɗan Takara a zaɓen Fidda Gwani yace sakamakon Zaben ya nuna cewa Tinubu shine wanda Jam’iyyar ke so.
“Ka kasance wanda yake da ɗumbin nasarori tare da cigaban Gwamnati da kuma ƙarfafa gwuiwa da ka nuna wajen yaƙi da cin mutuncin Dimokuraɗiyya a Najeriya, wanda hakan ya sanya ka zamanto wanda Jam’iyyar mu ta amince ma wa a zaɓen fidda Gwani.
Sakamakon Zaɓen Fidda Gwanin daya fito ya nuna cewa kaine wanda Jam’iyyar ta yadda domin Jagorantar Ƙasar nan.
Bani kokwanto akan matsayar da Deliget suka nuna wajen zaɓen ka a matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa.
Ina tayaka murna lashe zaben Fidda Gwani da kayi.