Daga Ranar Juma’a, Za’a Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin Najeriya Zuwa Ƙasa Mai Tsarki

Maninyata Aikin Hajjin Najeriya Zasu Fara Tashi zuwa Kasa Mai Tsarki, Daga Ranar Juma’a

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Babban Birnin Tarayya (FCT) za ta fara jigilar alhazai ta jirgin sama na rukunin farko na maniyyata zuwa kasar Saudiyya ranar Juma’a.

Don haka, hukumar ta umurci maniyyatan yankin da su kai je sansanin jigilar alhazai na dindindin da ke Bassan Jiwa, kusa da filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja.

Sanarwar da Daraktan Hukumar, Malam Muhammad Nasiru Danmallam ya fitar, ya ce sansanin na shirin shirya mahajjatan da za su yi jigilar su zuwa kasar Saudiyya.

Mallam Danmallam ya sanar da cewa, a ranar Juma’a ne aka shirya tashin jirgin farko na maniyyatan babban birnin tarayya Abuja, ya kuma bukaci wadanda ke cikin Shiri a jirgin na farko da su zo ranar Alhamis daga karfe 10 na safe domin karbar takardun tafiyar u da sauran shirye-shiryen jigilar.

Daraktan ya bayyana cewa, za a yi wa maniyyatan gwajin cutar Corona ne bisa ka’idojin aikin Hajjin bana da hukumomin Saudiyya suka yi, don haka ya shawarce su da su kai Isa filin jirgin saman domin gudanar da aikin tare da bin ka’idojin da aka gindaya.

Ya bukaci maninyata aikin hajjin na bana da su duba jadawalin tashin jirgin a babban ofishin hukumar da ke yankin, ko kuma a sansanin aikin Hajji na dindindin domin sanin jadawalinsu.

Ya ce hukumar ta dauki matakan tabbatar da bin duk ka’idojin aikin, kuma ta fara karbar bizar maniyyata a babban birnin tarayya Abuja na shekarar 2022, yayin da aka kammala shirye-shiryen bayar da tallafin tafiyar (BTA).

Wakilin majiyar Jaridar Jakadiya ya ruwaito cewa, kimanin mahajjata 2000 ne daga babban birnin tarayya Abuja ake sa ran za a jigilar su daga filin jirgin saman na Nnamdi Azikwe domin yin tafiyar ta bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram