Rushewar Bene Ya Hallaka Mutum 1, Da Jikkata Wani, A Kasuwar Kano

Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari

Wani Magini mai kimanin Shekaru 20 mai suna Abdulkadir Nasiru ya rasa rayuwarsa ,a yayin da abokin aikinsa Naziru Shafiu ya samu munanan raunuka, sakamakon rugujewar bene a kasuwar Kantin kwari dake Kano.

Biyu daga cikin ukku na ginin benen an kammala shi, a sa’ilinda ana cigaba da kashi na uku na ginin benen wanda ya rushe da misalin ƙarfe 12:35 na rana .

Wani daga cikin wanda ya shaida lamarin, yace mafi yawa daga cikin gine-ginen kasuwar, ba’a ginasu yadda ya kamata ba, ya kuma ƙara da cewa, mutane na ƙara gina shaguna ba’a kan tsari ba, ba kuma tare da shawarar masana ba.

A lokacin da yake shaidawa Vanguard Lamarin, mai magana da Yawun Hukumar Kashe Gobara na Jahar Kano, Yusuf Saminu, ya danganta lamarin ne akan rashin bin ƙa’ida wurin gina shaguna kamar yadda ya kamata.

 

A cewar sa “mun samu labari faruwar lamarin ne a jiya talata da rana, inda gini mai bene biyu wanda ba’a karasa ba suka rushe akan hanyar Unity dake kasuwar kantin kwari.

Lamarin ya rutsa da mutane biyu,wadanda suka hada da Abdulkadir Nasir mai kimanin shekaru Ashirin wanda ke cikin matsanancin Hali, sai kuma Naziru Shafi’u mai shekaru talatin wanda ya mutu. An kwashi gawar zuwa Asibitin kwararru dake Nasarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram