Ya Zama Wajibi Mu Hana PDP Dawo Wa Kan Karagar Mulki – Bola Tinubu

Ya Zama Wajibi Mu Hana PDP Dawo Wa Kan Karagar Mulki – Bola Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC a Kuma Dan Takarar jam’iyar a zaben shugaban kasa na 2023, Bola Tinubu, ya ce dole ne APC ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin jam’iyyar PDP ba ta yi nasara ba a zaben Mai zuwa.

A zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da aka kammala, Tinubu ya samu kuri’u 1,271 inda ya samu tikitin tsayawa takara.

Jam’iyyar ta Kuma bayyana da abokin hamayyarsa, Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri amatsayin na biyu, wanda ya samu kuri’u 316.

Yayin da Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya samu kuri’u 235, sai Kuma shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmad Lawan da ya samu kuri’u 152. Inda kuma Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya samu kuri’u 47.

Bayo Onanuga, Daraktan yada labarai da sadarwa na kungiyar yakin neman zaben Tinubu, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ruwaito dan siyasar da aka haifa a Legas yana fadin haka a jawabinsa na karbar tutar taka takarar jam’iyar.

Tinubu ya ce dole ne jam’iyyar ta yi aiki don ganin PDP ba za ta dawo kan karagar mulki ba bayan shafe shekaru 16 tana kan karagar mulki.

“Sun lalata mana tattalin arzikinmu. Sun bar ayyukan da aka fara. Ayyuka nawa da aka fara suka bari a baya? Dole ne mu nisantar da mabuɗin taskar mu daga gare su. Bai kamata a bar PDP ta dawo mulki ba,” inji shi.

Tinubu ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban kasa, Sanata Abdullahi Adamu, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, gwamnonin jam’iyyar APC, da ‘yan majalisar tarayya bisa goyon bayan da suka ba shi, yayin da ya kuma nuna matukar jin dadinsa ga hadin kan jam’iyar APC .

“Ina godiya ta musamman ga ’yan’uwana da suka yi takara a gare ni.” inji Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram