Yanzu-Yanzu: Atiku Ya Taya Tinubu Murnar Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC

Yanzu-Yanzu: Atiku Ya Taya Tinubu Murnar Lashe Zaɓen Fidda Gwani

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe Zaɓe Fidda Gwani da Jam’iyyar APC ta shirya.

Abubakar ya samu nasarar zama Ɗan Takarar Jam’iyyar PDP bayan an gudanar da Babban Taro a watan mayu, bayan kada Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike da Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Dr. Bukola Saraki da sauran su.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa ya wallafa a shafukan sa na zamani, domin taya tsohon Gwamnan Jahar Lagos murna, yana mai cewa zaɓen fidda Gwani na APC yana da wahala.

“Ina taya ka murna, akan samun nasarar ka a matsayin Dan Takarar Jam’iyyar ka. Kasha wahala,” ya bayyana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram