Yanzu-Yanzu: Bayan Lashe Zaben Tinubu, Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Wata Ganawar Sirri

Yanzu-Yanzu: Bayan Lashe Zaben Tinubu, Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Wata Ganawar Sirri

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, yana ganawa mai muhimmanci da gwamnonin jam’iyyar a Abuja.

An fara taron ne ‘yan mintoci kadan bayan fitowar tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023.

Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa zabin abokin takarar Atiku Abubakar ne zai jagoranci abubuwan tattaunawa a taron.

Akwai kuma wasu batutuwan da suka shafi kundin tsarin mulki na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan, da fitowar Tinubu da dabarun tunkude APC daga mulki a 2023.

Wasu daga cikin gwamnonin da suka halarci taron sun hada da gwamnan Bayelsa, Douyi Diri, gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, da na Benue, Samuel Ortom.

Sauran sun hada da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal da takwaransa na jihar Oyo Seyi Makinde

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram