Ƴan tawayen M23 Sun Farmaki Sojojin Majalissar Ɗinkin Duniya,Dana Tanzaniya
Akalla sojojin Tanzaniya guda uku da ke aiki tare da dakarun Majalisar ɗinkin Duniya a congo (Monusco) suka samu raunuka yayin wani artabu da sukayi da mayakan Yan tawayen M23.
Rundunar Sojin majalisar dinkin duniya tace an dauke sojojin guda uku izuwa birnin Goma domin cigaba da karbar magani bayan raunin da suka samu yayin fatawar da sukayi a sansanin su dake Rutshuru a arewacin yankin Kivu.
Bayanai daga rundunar sojin Congo sun tabbatar da cewa daya daga cikin sojojin kasar yaji mummunan rauni.
Kasar Tanzaniya na da sojojin fiye da ɗari takwas(800) da ke aikin wanzar da zaman lafiya tare da sojojin majalisar dinkin duniya a Jamhoriyar Dimokuraɗiyyar Kwango.
Mayakan M23 sun zargi sojoji da dakarun Majalisar Dinkin Duniya da bada fifiko ga yaki maimakon tattaunawar sulhu bayan da Sojojin suka kai wa mayakan farmaki a sansansu da ke Rutshuru.
To sai dai a wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun sojojin Dimokuraɗiyyar Congo a arewacin Kivu, Janar Sylvain Ekenge ya zargi ƙasar Ruwanda da tura wata tawagar sojojin ta musamman da yawansu ya kai 500 domin su taimakawa masu ta yarda kayar baya.
Amma kasar Ruwanda ta yi watsi da zargin, inda ta bayyana rikicin da ke faruwa a kasar Jamhoriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da matstalar cikin gida.
Sabon fadan dai ya kaure a ne a ranar Litinin din data gabata, bayan an shafe mako daya ba tare da wani tashin hankali ba a Rutshuru na larki Kivu.