Cutar Sanƙarau Ta Hallaka Ɗaruruwan Mutane A Jahar Jigawa

Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari

Kimanin mutane dari ne suka rasa rayukansu musamman ƙananan yara, ƴan Ƙasa da Shekaru 11, a sanadiyyar cutar sankarau a Jahar Jigawa.

Rahoton yanayin lamarin daga Jahar, ya bayyana cewa cutar ta fara yaduwa ne a watan da ya gabata, inda lamarin yayi ƙamari musamman a iyakokin Nijeriya da Nijar a jahar jigawa.

Bincike ya gano cewa, mutane da dama sun samu matasalar rashin ji,a ɓangare da dama na jahar sakamakon cutar .

Wasu Garuruwan da cutar ta shafa sun haɗa da, Mele, Dungundun,Kanya Arewa,Dantanoma dake kauyen Babura, Gumel, Maitagari sai kuma karamar hukumar Sulentankarkar
dake arewa maso yamma ta jahar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kimanin mutane Ɗari ne, suka mutu, a yayinda mutane dari- ukku da sittin da suka kamu da cutar a fadin jahar.

A yayin da Dagacin garin Dungundun, Malam Alkasim Yakubu yake bayani akan cutar, ya bayyana cewa mutane goma sha -tara ne suka mutu a kauyen kuma mafi yawancinsu ƙananan yara ne.

Ya Kara da cewa, cutar ta fara ɓulla ne daga watan Afirilu har Zuwa watan da ya gabata, lamarin ya cigaba da tsananta ne a yayinda cutar da rasa rayuka suka yi ƙamari.

Malam Yakubu ya cigaba da cewa, “a sanadiyyar cutar, mutane goma sha -tara suka mutu, sai kuma mutane biyu suka kamu da cutar kurumta.

malam yakubu yace sun ɗauki mutanen da suka kamu da cutar Zuwa asibitin garin Danladi Gumel, a sa’ilinda wasu suka mutu tun kafin zuwa, saura kuma ana cigaba da kula dasu, yana mai cewa basu taba fuskantar irin wannan annoba ba.

Mai garin kauyen Bulama a Kauyen Mele dake karamar hukumar Gumel, Malam Yusif Ahmad,inda yake cewa mutum Ashirin suka mutu.

Sai kuma Dagacin garin Kanya Arewa dake karamar hukumar Babura ,Alhaji Akilu Dawaki ya bayyana cewa mutane sha-tara ne suka mutu a yankin nasa sai mutane 70 suke fama da cutar.

A cewar sa, “abinda ya taimake wajen shawo kan cutar shine, gaggawar samar da wurin kebe mutanen da suka kamu da cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram