FG ta bada hutun ranar Litinin domin bikin ranar Dimokuraɗiyya ta Shekarar 2022
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin 13 ga watan Yuni na shekarar 2022 a matsayin ranar hutu z domin bikin ranar Dimokuraɗiyya ta wannan Shekarar.
Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola ya bayyana haka a madadin Gwamnatin Tarayya, a cikin wata sanarwa daya fitarwa Kafafen Yaɗa Labaru a ranar Alhamis.
Ya taya ƴan Najeriya murna akan wannan rana, tare da yin kira a garesu dasu goyi bayan wannan Gwamnati a ƙoƙarin ta na samar da tsaro, haɗin kai da zaman lafiya.
“A yayinda muka shaida ranar Dimokuraɗiyya ta Duniya a tarihin ƙasar mu, muyi ƙokari mu riƙa aiki da abinda iyayen mu na kasa suka yi, tare da tabbatar da cewa Najeriya ta zamo mai haɗin kai, tsaro, da zaman lafiya.
Ministan yayi kira ga ƴan Najeriya dasu yi amfani da Manhajar da aka fitar wanda za’a yi amfani da’ita domin magance matsalolin tsaro da sauran bala’o’i a Ƙasar.
Ya bada tabbacin cewa da namijin ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari keyi na tsare rayuka da Dukiyoyin Al’umma, da Tattalin Arziki, Ƙasar zata cigaba da samun cigaba.