Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 murna.
Shugaban ya aike da sakon ne ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu a ranar Laraba.
Shugaban ya bayyana cewa bayan samun nasara, Tinubu yana da cikakken goyon bayansa.
Ya ce, “Yanzu dole ne jam’iyyar mu ta hada kai a bayan dan takararmu domin samun nasara a zaben 2023 domin gwamnatinmu ta ci gaba da tabbatar da tsaron al’ummarmu da bunkasa tattalin arzikinmu da kuma ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa.
“A lokacin zabukan fidda gwani, an samu bangaranci da rashin jituwa a tsakanin ‘yan takara kuma yanzu da tsarin ya kare dole ne mu samar da hadin kai a jam’iyyarmu.
Ta haka ne jam’iyyar APC za ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da za ta fi dacewa da al’ummar Nijeriya. Yanzu lokaci ya yi da za mu sanya tsarin a baya.
“Saboda abin da za mu iya yarda da shi shi ne, APC ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da za ta fi dacewa da abubuwan da al’ummar Nijeriya suka sa a gaba. Amma hanyar da za mu nuna cewa za mu iya ci gaba da wannan aikin shi ne haɗin kai.
“Motsin da muka kirkiro a 2013 ya wuce daidaikun mutane. A tare, mun kafa tarihi inda muka zama jam’iyya ta farko a tarihin kasarmu da ta kawar da jam’iyya mai mulki tare da shigar da dan takararmu zuwa Shugaban kasa ta hanyar mika mulki cikin lumana ta hanyar dimokuradiyya.
“Muna da yakinin Bola Ahmed Tinubu zai kiyaye tare da inganta wannan nasara ta dimokuradiyya da kuma abin da ya bari, shi ne dan takarar da ya dace da muradin Najeriya domin shi ne dan takarar jam’iyyar APC kuma a karkashin jam’iyyarmu ta ci gaba da gudanar da mulkinta, Nijeriya za ta iya samun daukaka da cika alkiblarta a Afirka da ma Duniya.
“Babban abin da ya faru a wannan babban taron jam’iyyarmu shi ne kuzarin ‘yan takarar shugaban kasa kuma daga cikinsu ne muka zabi shugaba mafi farin jini.
“Na gane kuma na yaba da kishi da yarda da kai a tsakanin maza da mata na jam’iyyarmu.
“Ina kuma gode wa wakilan da suka yanke shawara mai kyau da ta kai ga fitowar dan takararmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.”