Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Ta Ƙasa

A halin yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron majalisar tsaro ta kasa a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Taron da ake gudanarwa a zauren majalisar ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya; Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, shugaban rundunar sojojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo, shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman.

Kazalika sauran sun hada Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram