Zan Yiwa Atiku, Tinubu Ritayar Siyasa A 2023 – Moghalu na Jam’iyyar ADC

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Farfesa Kingsley Moghalu, ya sha alwashin kawar da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar; da takwaransa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ta hanyar yi musu murabus na dindindin daga harkokin siyasa.

Moghalu, wanda mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya ne, ya ce zai yiwa su biyun ritaya ta hanyar kayar da su a zaben badi.

Moghalu ya yi magana ne a Abeokuta, jihar Ogun, ranar Laraba, a yayin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar ADC.

Akalla ‘yan takara 10 ne suka fafata da wakilai 2,100 a zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC da ya gudana a Abeokuta domin neman tikitin takarar jam’iyyar.

Moghalu da kuma wanda ya kafa gidan Talabijin na Roots Television Nigeria, Dumebi Kachikwu, su ne kan gaba a fafatawar neman tikitin jam’iyyar ADC.

Sauran ‘yan takarar sun hada da Dr. Mani Ibrahim, Joyce Nsaka, Dr. Chike Okogwu, Dr Chukwuka Monye, ​​Angela Johnson, Chichi Ojei, Dr. Muhammed Lamido, Bishop Ify-George Oforkansi, Dr. Favor Ayodele, Ebiti Jegede da sauransu.

Kazalika Moghalu ya ce “Na zo ne don in ba da kaina gare ku ba don na fi kowa a nan ba amma don in kula da makomar kasarmu. Na bayar da kaina ne saboda Allah ya ba ni babban goyon baya na tsayawa kafada da kafada da Atiku, Tinubu tare da yi musu ritaya.”

Ya yi alkawarin sanya ‘yan Najeriya yin alfahari idan aka zabe shi shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram