Dalilan Da Suka Sanya Na Kori Malamai 1000 — Inji Soludo

Dalilan Da Suka Sanya Na Kori Malamai 1000 — Inji Soludo

Gwamnan Jahar Anambra Farfesa Charles Soludo yace kimanin Malaman Makaranta 1,000 aka kora daga aiki, domin an ɗauki basu cancanta ba.

Gwamnan yace waɗanda aka koran basu cancanta su riƙa koyarwa ba.

Soludo ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Sakataren Ƴan Jarida na Gwamnan Mr Chris Aburime ya Fitar a ranar Alhamis.

A cewar sa babu wani Malamin Makaranta daya cancanta da aikin, kuma Gwamnatin Jahar Anambra ace ta kore shi.

Sanarwar tace “hankalin mu yakai ga wani bayanai na zanga-zanga da Kungiyar Iyaye da Malamai suka yi, na zargin korar Malamai masu aiki na Din-Din-Din.

 

“Domin magance duk wani ruɗani, babu wani Malami daya cancanta wanda aka kora daga aikin sa.

“Domin malaman an ɗauke su ne kawai don ana sauri ayi abubuwan da basu kamata ba, wanda Gwamnatin data gabata tayi.

“An kuma buƙace su dasu tabbatar da ƙwarewar maluntar su, ta hanyar gudanar da Jarabawa.”

Gwamnatin Anambra dai tuni ta sanar da guraben ɗaukar Malamai da Ma’aikatan Lafiya guda dubu 5,000, inda sama da mutane dubu 31,500 zasu zana Jarabawar.

Za’a gudanar da Jarabawar a ranar Asabar mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram