Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa reshen Jahar Osun, ta bayyana cewa mutane bakwai sun rasa rayukansu sakamakon hadurran da akayi a watan mayu.
Kwamandan Shiyya na Hukumar, Paul Okpe, ya bayyana hakan ne, a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun sa Agnes Ogungbemi ya fitar.
Okpe ya ce,hadduran guda ashirin da shidda da aka samu, a titina daban-daban, sun yi sanadiyyar rasa rayukan mutane bakwai, yayin da sauran mutane Ashirin da shidda suke fama da jinya.
A cewar sa, hukumar ta kama mutane dari-ukku da saba’in da biyar wadanda basu bin ka’idar tuki a fadin jahar,a sa’ilinda mutane dari-da ashirin da biyar aka ilmantar dasu akan doka ta hanya.
Okpe ya ce hukumar ta bada lasisin tuki ga masu motoci, amma har yanzu akwai wanda basu karɓa ba.
“kimanin wanda suka karɓi lasisin da wadanda basu karba ba a watan Mayu, sun kai kimanin mutane dubu hudu da saba’in da hudu,” Inji