Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Dan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC Kuma Tsohon Gwamnan Jahar Lagos, Asiwaju Bola Tinubu na ganawar sirri tare da Gwamnan Jahar Kogi Yahaya Bello, akan abinda masana siyasa suka bayyana cewa, wani yunƙuri na yin sasanci da ƴan Takarar APC da suka nemi takara
Tinubu yayi ganawar Sirrin a yau Juma’a, bayan ya samu rakiyar Gwamnan Jahar Lagos, Babajide Sanwa-Olu, da Gwamnan Jahar Zamfara Bello Matawalle, da kuma Gwamnan Jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Tsohon Gwamnan Jahar Edo, da Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, na daga cikin ƴan tawagar.
Amma babu tabbacin idan samun Abokin Takarar Tinubu na daga cikin abinda za’a tattauna.
Jaridar PUNCH ta lura cewa, zasu yiwa Manema labaru jawabi akan dalilin taron sirrin.