Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Makasan Ɗiyar Shugaban Ƙungiyar Yarbawa Ta Afenifere

Wata babbar kotu a jihar Ondo ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa bisa samun su da laifin kashe Misis Funke Olakurin, diyar shugaban kungiyar Afenifere mai fafutukar kare al’ummar kabilar Yarbawa, Pa Reuben Fasoranti.

Wadanda aka yanke wa hukuncin, Muhammed Shehu, Mazaje Lawal, Adamu Adamu, wadanda kuma aka zarge su da laifin kashe wani mafarauci a dajin an same su da dukkan tuhume-tuhumen da aka yi musu.

Alkalin kotun, Mai shari’a Williams Rotimi Olamide a hukuncin da ya yanke ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma bindige su bisa zargin da suka hada da hada kai na kisa, kisa, garkuwa da mutane, da kuma fashi da makami.

A ranar 12 ga watan Yulin shekarar 2019, Olakurin, mai shekaru 58, ta nufi Akure, jihar Ondo, daga Legas, lokacin da wasu makiyaya suka kai mata hari suka harbe ta a kan hanyar Benin zuwa Sagamu.

Bayan an kwashe watanni ana bin diddigi da bincike, an kama wadanda suka kashe ta a ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 2020, daga hannun jami’an runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami ta rundunar ‘yan sandan Najeriya.

A halin da ake ciki kuma, wanda ake tuhuma na hudu, Auwalu Abubakar, wanda ake zargi da bada taimako, alkalin kotun ya sallame shi.

Mai shari’a Olamide wanda ya jajanta wa iyalan mamacin ya bukaci gwamnati da ta gaggauta yin wani abu game da karuwar rashin tsaro a kasar wanda a cewarsa ya sa mutane da dama suna biyan kudin sabulu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram