Ƴan Bindiga Sun Hallaka Shugaban Matasan Jam’iyyar APGA A Anambra
Wasu ƴan bindiga dake addabar Jahar Anambra, sun hallaka Shugaban Jam’iyya mai Mulki ta APGA a Jahar.
A cewar majiyoyi, Shugaban Matasan da ake kira da Emeka Alaehobi an sace shi a gidan sa dake Ukpor Karamar Hukumar Nnewi ta Jahar, kwanaki biyu da suka gabata.
Ƴan bindigar sun kasance basu kira waya ba, har zuwa lokacin da aka ga gawar sa a ranar Asabar da safe a makwabtan garin mai suna Utuh.
Majiyar tace “shine Emeka Alaehobi, Shugaban Matasa na Ƙaramar Hukumar Nnewi ta Kudu. An sace shi kwanaki biyu da suka gabata.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar DSP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da cewa an ga gawar ne a yankin a ranar Asabar, amma ba’a gano ko ta wace ce ba.
Yace “a lokacin da Jami’an mu suka je wurin, wasu mutane sun ɗauke gawar, har yanzu bamu gano ba, amma mun gane cewa Ashe gawar ta Shugaban Matasa ce.”
Ukpor yankine a Ƙaramar Hukumar Nnewi da ya kasance yanki mai matsala, tun bayan da Ƙungiyar IPOB ta fara gudanar ta’addancin ta.