Ƴan Bindiga Sun Sace Matasa 15 A Imo

Wani lamari maras dadi ya faru yau Asabar bayan da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka afkawa al’ummar Ekwe a karamar hukumar Isu ta jihar Imo inda suka yi awon gaba da wasu matasa maza 15 a yankin.

‘Yan bindigar sun afkawa al’ummar ne ta kogin Njaba da ya raba yankin Ekwe daga al’ummar Amucha da ke karamar hukumar Njaba, kamar yadda wani shugaban al’ummar yankin ya bayyana.

Wani dan kabilar Ekwe, Akubuo Princewill, ya shaida cewa, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu matasa 15 da suke hako yashi a kogin Njaba.

Akubuo ya ce ‘yan bindigar sun yi harbi sama ba kakkautawa kuma suna neman karin matasan al’ummar da za su yi garkuwa da su.

Ya ce wasu samari da wasu ‘yan yankin suka hango su daga nesa sun kutsa cikin dazuzzukan da ke kusa da su domin tsira daga sace su.

Akubuo ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo dauki ga al’umma duk da cewa yana mamakin abin da zai iya sanar da mamayar al’ummar.

Ya ce, “Muna kira ga gwamnan jihar, Sanata Hope Uzodimma da ya kawo mana dauki.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Michael Abattam, ya shawarci al’ummar yankin da su kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda da ke yankin domin baiwa ‘yan sanda damar shawo kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram