Ƴan Majalisar APC 8 A Jahar Kebbi Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kebbi ta samu sabbin ‘yan majalisa takwas daga jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki.

Sabbin ‘yan majalisar dai sun hada da ‘yan majalisar tarayya biyar da kuma ‘yan majalisar jiha uku.

An yi zargin cewa tsarin da jam’iyyar APC ta gudanar da zabukan jihar ne ya sa ‘yan jam’iyyar suka fice daga jam’iyyar inda da yawa daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar suka yi zargin cewa an yi watsi da su.

A majalisar tarayya, sanata mai wakiltar mazabar Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero; Sanatan Kebbi ta Arewa, Yahaya Abdullahi; Shugaban majalisar dattawa, ciki har da dan majalisar wakilai, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP. Haka kuma, mambobin mazabar Aliero/Jega/Gwandu da Dandi/Arewa na tarayya, Mohammed Jega da Abdullahi Zumbo, sun fice daga APC zuwa PDP.

A majalisar dokokin jihar, Habibu Labbo, Ismaila Biu, da Mohammed Aliero, masu wakiltar mazabar Gwandu, Arewa, da Aliero, suma sun fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Kebbi, Usaini Raha, ya tabbatar da ficewar ‘yan majalisar zuwa jam’iyyar.

Idan ba’a manta ba ko a makon da ya gabata Jaridar Dimokuradiyya ta kowo rahoton yadda Sanata Aleiro ya fice a jam’iyar ta APC inda ya koma jam’iyar PDP Kuma ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram