Da Ɗuminsa: Ƴan Ta’adda Sun Saki Wasu Fasinjan Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna

Ƴan Ta’adda Sun Saki Wasu Fasinjan Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna

Ƴan Ta’addan da suka kai hari a Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2022, sun saki wasu dake hannun su.

Ƴan Ta’addan sun ɗana Bam a kan hanyar jirgin, wanda ya sanya dole Jirgin ya sauka daga kan hanyar, a yayinda suka buɗe wuta ga wasu, tare da Hallaka Mutane 9 da sace mutane 62, ciki har da yara da manyan mutane.

Daily Trust ta bada rahoton cewa bayan sun shafe kwanaki 74 a hannun ƴan ta’addan, sun saki mata 6 da maza 5 a ranar Asabar, biyo bayan tattaunawar da akayi dasu.

Mawallafin Jaridar Desert Herald Tukur Mamu wanda ya kasance mai yin sulhun, ya tabbatar da sakin Matafiyan.

Yace majiyoyin sa, sun tabbatar masa cewa sun saki namiji dake fama da rashin lafiya, yana mai ƙara dacewa mata suna daya daga cikin wanda suke hannun su.

“Nayi tunanin zasu saki dukkanin matan a kashi na farko a yayin da tattaunawa akan sako wadancan zai cigaba, amma sun rage yawan matan da zasu sako saboda Gwamnatin Najeriya dasu saki waɗanda ke fama da rashin lafiya.”

Wasu daga cikin ƴan uwan waɗanda aka sacen, sun shaidawa Majiyar Jaridar Jakadiya cewa suna saran za’a sako dukkanin waɗanda ke a tsare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram