Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa (Cigarin Musawa) ya gargadi duk wani mai riƙe da wata kujera ko mai neman wata kujera a ƙarƙashin Jam’iyyar APC a jihar Katsina da ya halarci wani taro ko gangami da ake zagi ko aibata shugaban kasa Muhammadu Buhari da adalin gwamna Alhaji Aminu Bello Masari, Jam’iyyar APC a jihar Katsina za ta kore shi, idan kuma wani mukami ya ke nema za ta tabbatar bai yi wa Jam’iyyar takara ba a zaɓen shekarar 2023.
Alhaji Bala Abu Musawa ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da wasu asibitoci da tituna da matashin dan kwangilar nan, dan asalin karamar hukumar Malumfashi ya gina a mahaifarsa, Alhaji Muntari Sagir da Gwamna Aminu Bello Masari ya jagoranci kaddamar wa yau Asabar a garin Malumfashi ta jihar Katsina.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Katsina, wanda ya wakilci Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Katsina a wajen taron ya ce Jam’iyyar APC ta gudanar da zaɓukan fitar da gwani a matakai Daban-daban a wani wuri mun yi dai-dai ba kuma a rasa wurin da muka yi kura-kurai na ajizanci. Abubuwa da ke faruwa bayan kammala zaɓukan, Jam’iyyar APC zaune lafiya take kuma ba mu tunanin faɗuwa Zaɓe saboda mun tsaida nagartattun yan takara a matakai daban-daban.
Alhaji Bala Abu Musawa (Cigarin Musawa) ya kara da cewa Jam’iyyar APC a jihar Katsina ba za ta zura ido ba ga duk wani zababbe ko wani dan majalisa ko shugaban karamar hukuma ba ko mai son tsaya wa takara ba, ya halarci wani taro da ake zagi ko aibata shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello ba, za mu dauki kwakkwarar Mataki kansa na kora komin girmansa.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa ya cigaba duk wanda ya faɗi zabe idan har ya yarda da Allah ya taho ayi wannan tafiya da shi, idan kuma ya ji bai iyawa to ya yi zamansa, Saboda ko da shi ko babu shi ina da yakinin Jam’iyyar APC za ta ci zabenta da yardar Allah a shekarar 2023