Hana Okada: Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Acaɓa 50, Bayan Sun Farma Ke Su A Lagos

Hana Okada A Legas: Yan sanda Sun Kama Mutum 50, Yayin da Matuka Mashin Suka Farmakesu A Ikorodu

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas na ci gaba da aiwatar da dokar hana babura na haya.

Gwamnatin Legas ta haramta gudanar da ayyukan okada a manyan tituna da kuma a kananan hukumomi shida dake jihar.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Apapa, Eti Osa, Ikeja, Lagos Island, Surulere, da Legas Mainland.

A ranar Asabar, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin, ya bayyana yadda ‘yan sanda suka kai samamen kama wadanda suka karya Dokar a daren Juma’a a Ikorodu.

Kakakin ya ce ‘yan bindiga ne da mahaya da kuma matuka suka fafata da ma’aikatan da suka yi kokarin hana su taka dokar.

Hundeyin ya kara da cewa an kai samamen ne bayan rahotanni da dama kan masu tuka babura da ke aiki da daddare.

“Mun sake duba dabarunmu kuma muka Kai samame a Ikorodu a daren jiya (wanda aka haramta a duk manyan tituna).

“Mahaya da wasu Yan daban sun kai wa ‘yan sanda hari. An kama mutum 50 daga cikin su, an kama babura 14.”

Kazalika jami’in ya kuma bayyana cewa mataki na gaba shine murkushe baburan da aka kama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram