Na Koyi Darasi Daga Cikin Darussan Da Tinubu Ya Koyaman — Gwamna Yahaya Bello

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a ranar Juma’a ya shaidawa Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, cewa ya koyi abubuwa da yawa daga karamar laccar da ya yi masa.

Bello ya bayyana haka ne a lokacin da Tinubu ya kai masa ziyara a Abuja, sa’o’i 72 da fitowar tsohon gwamnan jihar Legas a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.

Ya kuma bayyana cewa ya ruguje majalisar yakin neman zaben shugaban kasar sa kuma zai bayar da ginin ga kungiyar yakin neman zaben Tinubu.

Ku tuna cewa Tinubu ya kayar da irin su Bello, Rotimi Amaechi, da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da dai sauransu, a yayin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC a Abuja ranar Laraba.

Bello ya ce, “A yau na ruguje kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa ta. Na bayar da gudummawar sakatariyar kungiyar kamfen a gare ku. Na koyi abubuwa da yawa daga ƙaramar laccar da kuka yi mana.

“Abin da dattawa suka hango lokacin da suke cikin kwari, ƙananan ba za su gani ba.”

Bello ya lura da cewa zaben fidda gwani ya zo ya kuma yi alkawarin jagorantar matasa wajen yi wa Tinubu yakin neman ganin APC ta samu nasara.

“ PDP ba za ta sake shugabancin kasar nan ba. Na gode dukkan abokan aikina gwamnoni da suka ba ni damar yin koyi da ku.

“Sanata Abdullahi Adamu (shugaban APC na kasa) bai taba faduwa zabe ba, kuma za mu ci zaben 2023. Taron namu ya gudana lafiya da kwanciyar hankali,” Bello ya kara da cewa.

Tinubu ya samu rakiyar gwamnoni uku – Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Abdullahi Ganduje (Kano) da Bello Matawalle (Zamfara).

Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, shi ma ya je wurin taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram