2023: Ni Zan Jagoranci Ganin APGA Ta Lashe Zaɓen Gwamnan Abia — Inji Gwamnan Anambra
Gwamnan Jahar Anambra ya sha alwashin Jagorantar ganin cewa Jam’iyyar APGA ta samu nasarar lashe Zaɓen Shekarar 2023 na Gwamna a Jahar Abia.
Soludo ta bayyana haka a ranar Asabar a lokacin da Ɗan Takarar Gwamna a Jam’iyyar APGA a Jihar Abia, Farfesa Gregory Ibe, ya kai kashi ziyara a gidan Gwamnatin Jahar Anambra.
Da yake yabawa da kyawawan Ɗabi’un Ibe, Soludo ya bayyana shi a matsayin wanda ya cimma nasarori kuma Ɗan Abia da Ndigbo.
“Gudunmuwar da Farfesa Greg ya bayar wajen cigaban Al’umma, abune daya cancanci yabawa. Tabbas Abia na bukatar mutum kamar Greg Ibe. Dole muje Abia domin tunkarar zaben idan lokaci yazo”, Inji Soludo.
Soludo yace yanzu Lokaci daya kamata yankin Kudu Maso Gabas su amince da APGA domin samun cigaba.
A cewar sa, yanzu lokaci ne da Ndi Igbo ya Kamata ta gane kanta, domin yanzu zaɓe ana samun sa ne ta hanyar bin hanyoyi da aka amince dasu.
Gwamnan yayi kira gasu ƴan Kudu maso Gabas dake a wasu Jam’iyyun, dasu dawo Jam’iyyar APGA domin bunkasar cigaba.
Yace tarin ƙuri’u na yankin Kudu maso yammaci da Arewa maso Yamma, banda wannan babu wani wuri.
Soludo ya taya Ibe murnar shigowa Jam’iyyar APGA yana mai bayyana haka a matsayin abin cigaban Ƙasa.