Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa na yawaitar matsalar tsaro a Kasar, yana mai cewa baya iya runtsawa kan matsalolin a kullum.
Ya bayyana haka a cikin jawabin da ya yiwa ƴan Kasar a ranar Lahadi.
A lokacin da yake baiwa ƴan Najeriya tabbacin cewa Gwamnatin sa na bakin Ƙoƙari wajen magance matsalolin tsaro, ya yi kira a garesu dasu zama masu Addu’o’i.
“A wannan rana ta musamman, ina so mu riƙa addu’a ga dukkanin wanda iftila’in ta’addanci ya shafa a cikin Addu’o’in mu. Ina damuwa matuƙa, da dukkanin wanda ya shafa, da Wanda aka kama a dalilin ta’addanci da garkuwa da mutane. Ni da Jami’an tsaro muna yin dukkanin abinda zamu iya domin ganin mun magance ƴan Ta’adda.
“Ga waɗanda suka rasa rayuwar su, zamu cigaba da neman adalci daga wadanda suka aikata. Da wanda suke hannun su, bazamu gajiya ba har sai an sake su, kuma an magance ƴan Bindigar. Idan muka haɗa kai, zamu samu nasara akan ƴan ta’adda da aikace-aikacen su.
“Mun sake yin canje-canje akan tsari na wasu Jami’an tsaro. Wasu daga cikin makamai da muka siyo, sun zo gida Najeriya, kuma tuni an tura su a wuraren da zasu fara aiki.
“An ɗauka darajar Harkokin sadarwa da kula da bincike domin inganta kwazo na gano ƴan Ta’adda. Muna ɗauka sabbin jami’an tsaro tare da horas da wanda muke dasu domin inganta tsaro.